ICC za ta kama tsohon shugaban 'yan sandan Philippines Rosa
May 11, 2026
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC da ke birnin The Hague, ta ba da umarnin kama tsohon shugaban 'yan sandan Philippines, kuma 'dan majalisar dattijai a yanzu, Ronald Dela Rosa, bisa zargin kisan dubban jama'a.
Karin bayani:An tsige mataimakiyar shugaban Philippines Sara Duterte
ICC na kallon Dela Rosa, a matsayin kanwa uwar gami, wajen aiwatar da shirin da shugaba Rodrigo Duterte ya bijiro da shi, na yaki da safarar muggan kwayoyi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutanen da ba-su-ji-ba-ba-su-gani-ba.
Karin bayani: Za a fara shari'ar tsohon shugaban Philippines a kotun ICC
A watan Maris na 2025 'yan sandan Philippines, bisa hadin gwiwar na kasa-da-kasa interpol, suka kama tsohon shugaban kasar Rodrigo Duterte, sannan suka mika shi hannun kotun ICC, kan zargin kashe mutane 6,252, daga ranar daya ga watan Yulin 2016, zuwa 31 ga Mayun 2022, da sunan yaki da miyagun kwayoyi a kasar.