Iraki za ta fi ko'ina shan wahalar yakin Iran
March 5, 2026
Yayin da rikicin Iran da abokan hamayyarta ke kara kamari a Gabas ta Tsakiya, kasar Iraki na fuskantar barazana daga tasirin yakin kai tsaye. Ana dai gargadin cewa rikicin na iya tayar da tsohon tabo na bangaranci, tare da shafar tattalin arziki da siyasar kasar.
Iraki ita ce kasa daya tilo a Gabas ta Tsakiya da hare-haren bangarorin biyu a Iran suka shafa. Masana na gargadin cewa wannan yakin na iya sauya siyasarta, ya kuma kara rura wutar rikicin bangaranci, har ma ya shafi albashin miliyoyin ma'aikatan gwamnati. Wasu mazauna kasar na cewa tsohon sabanin da ke tsakanin mabiya mazhabar Sunni da Shi'a, rikicin da kusan ya jefa kasar cikin yakin basasa shekaru kusan ashirin da suka wuce, na sake bayyana.
Ga ‘yan kasar Irakin, duk abin da ya faru a Iran ba iya Iran din kadai yake shafa ba. Kasashen biyu na da iyaka mai tsawon kusan kilomita dubu daya da dari biyar, baya ga alakar kasuwanci da siyasa mai karfi a tsakaninsu.
Baya ga rikicin tsaro, masana na cewa tattalin arziki ma na iya fuskantar matsala. Kasuwanci tsakanin Iran da Iraki ya kai na kimanin dala biliyan 12 a shekarar 2024, yayin da Iran ke samar wa Iraki kusan kashi daya cikin biyar na kayayyakin masarufi da ake amfani da su a kasar. Haka kuma Iran na daga cikin manyan kasashen da ke samar wa Iraki makamashi.
A lokutan rani a Iraki, yawan katsewar wuta kan haddasa zanga-zanga daga jama'a. A shekarar 2023, iskar gas daga Iran ta taimaka wajen samar da kusan kashi 30 cikin 100 na wutar lantarkin Iraki. Sai dai wasu masana na ganin cewa ‘yan Iraki sun saba da fuskantar irin wadannan kalubale.
Wani mai bincike mai zaman kansa a Baghdad, Hamzeh Hadad, ya ce babbar barazana za ta bayyana ne idan yakin ya dauki lokaci mai tsawo.
Tattalin arzikin Iraki dai ya dogara sosai da kudaden da take samu daga sayar da man fetur. Idan kuma rikicin ya kawo cikas ga zirga-zirgar tankokin mai ta mashigar Hormuz, kudin shiga na gwamnati na iya raguwa sosai. Hakan kuma na iya shafar albashi da fansho da gwamnati ke biya wa kusan mutane miliyan bakwai a kasar.
A bangaren siyasa ma, rikicin na iya sauya lissafi a Baghdad. Har yanzu Iraki na kokarin kafa sabuwar gwamnati bayan zaben da aka gudanar a karshen shekarar da ta gabata, yayin da tattaunawar siyasa ta tsaya cak sakamakon sabani kan wanda zai zama firaminista. Kuma raunin tasirin Iran na iya sauya wannan lissafi.