1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceChaina

SIPRI: Yaushe za a rage cininkin makamai?

April 28, 2026

Shekaru 11 a jere ke nan ana samun karuwar kudin da ake kashewa kan al'amuran soja a duniya, shekara da 2025 ta kasance wacce aka fi kashe makudan kudi a fannin na soja.

https://p.dw.com/p/5Cy1C
SIPRI | Duniya | Yaki | Soja | Kudi | Zaman Lafiya
Kayan yaki na lakume makudan kudi a duniyaHoto: picture alliance/dpa/dpa-Zentralbild

Cibiyar Bincike kan Zaman Lafiya ta Kasa da Kasa da ke birnin Stockholm na kasar Sweden wato SIPRI ta ce dalar Amurka trillion 2000 da miliyan 887 wajen sayen jiragen yaki na ruwa da na sama da makamai ciki har da masu linzami, inda ta alakanta hakan da yadda kasashe ke mayar da martani a kan yaki da matsaloli da kuma rashin tabbas a wasu yankunan. SIPRI ta nunar da cewa, an ci gaba da gwabza yaki a Ukraine da Gaza a 2025 kana rikice-rikice kamar yakin Sudan sun kara ta'azzara rashin tabbas a duniya.

Yiwuwar karuwar kashe kudi a fannin soja

Xiao Liang da ke bincike a bangaren kudin da aka kashe a aikin soja a cibiyar ta SIPRI ya nuna fargabar cewa: "Ganin yadda ake ci gaba da samun rigingimu a kasashen duniya da dama, akwai yiwuwar batun kashe kudin a fannin sojan ya dora har gaba da shekara ta 2026 da muke ciki. Binciken na SIPRI ya nunar da cewa, kasashen Turai sun fi kashe kudi a fannin na soja a shekara ta 2025 da ta gabata. SIPRI ta ce, kudin da kasashen Turan suka kashe ya karu da kaso 14 cikin 100 da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 864.

SIPRI | Xiao Liang | Yaki | Soja | Kudi | Zaman Lafiya
Mai bincike kan kudin da ake kashewa bangaren soja a Cibiyar SIPRI Xiao LiangHoto: DW

Yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine a shekara ta 2022, ya haifar da fargaba a mafi yawan kasashen Turai kan yiwuwar samun barazana daga Moscow. Wannan fargaba ta sanya kasashen musamman mambobin kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO, kara adadin kudin da suke kashewa a fannin tsaro. A cewar Xiao Liang mai bincike a bangaren kudin da aka kashe a aikin soja a cibiyar ta SIPRI, kasashen tsakiya da yammacin Turai ne suka fi kara yawan kudin da suke kashewa a fannin na tsaro.

Karin Bayani: Kasashe na kara kashe kudi kan makamai

Ga misali kasar Spaniya ta kara kasafinta a fannin tsaro da kaso 50 cikin 100, yayin da Poland ta kara nata da kaso 23 cikin 100 Italiya kuma ta kara da kaso 20 cikin 100. Jamus ce kan gaba a kashe kudi a fannin soja, a shekara ta 2025 da ta gabata. Ta kara kasafin kudinta a fannin da kaso 24 cikin 100 zuwa dala biliyan 114, abin da ya sanya ta zama kasa ta hudu a duniya. A karon farko tun shekara ta 1990, Jamus ta kashe kaso biyu da digo uku cikin 100 na arzikin kasarta wanda ya haura adadin da NATO ta kayyade na kaso biyu cikin 100.

Kokarin rage dogaro da Amurka?

A cewar Liang koda yake ba ya tunanin karfin sojojin Jamus na karuwa cikin hanzari kamar yadda ake kashe musu kudi, amma yana tunanin sannu a hankali Jamus na zama mai dogaro da kanta a fannin soja. Ba ya ga yakin Rasha da Ukraine, rashin tabbas kan yiwuwar ci gaba da huldar tsaro da Amurka na daga cikin abin da ya sanya Jamus kara yawan kudin da take kahewa a fannin sojan. Kamar sauran kawayenta na NATO, Jamus na kokarin rage dogaro da Amurka musamman yadda Shugaba Donald Trump ke ci gaba da sanya alamar tambaya a kan yiwuwar dorewar dangantakar tsaro a tsakaninsu.

SIPRI | Jamus | Yaki | Soja | Kudi | Zaman Lafiya
Jamus na kan gaba a Turai, wajen kara yawan kasafin kudi a fannin sojaHoto: Philipp Schulze/dpa/picture alliance

Abin da ya fi bayar da mamaki shi ne, Amurka ba ta kashe kudi mai yawa ba a fannin na soja bara. Binciken SIPRI ya nunar da cewa, dalar Amurka biliyan 954 kacal ta kashe wato kaso bakwai da digo biyar cikin 100 kasa da abin da ta kashe a 2024. Hakan ba ya rasa nasaba da yadda majalisar dokokin Amurkan, ta ki amincewa da sabon tallafin soja ga Ukraine. Sai dai abin ya fara sauyawa a bana, sakamakon yakin Gabas ta Tsakiya da kuma karuwar fargaba a Asiya.

Karin Bayani: Amurka ke kan gaban wajen sayen makamai

Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta  ce, kwanaki shida kacal na farkon yakin Iran a wannan shekara ta 2026 da muke ciki ya lakume dalar Amurkan biliyan 11 da miliyan 300. Washingtong dai ta ci gaba da kasancewa ta kan gaba wajen kashe kudin a fannin soja, yayin da Chaina ta rike kambunta na take mata baya a matsayin kasa ta biyu a duniya baki daya. Rasha ce ke matsayi na uku Jamus ta hudu, kana Indiya ke take masu baya a matsayi na biyar.

 

Fassara da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani