Rikice-rikicePakistan
Iran: Ziyarar babban jami'in tsaron Pakistan
May 22, 2026
Talla
Pakistan da ke zaman makwabciya kana kawa ga Tehran, ta jima tana kokarin shiga tsakanin da nufin kawo karshen yakin da Iran din ke fafatawa da kasashen Amurka da Isra'ila. A nasa ran Field Marshal Asim Munir zai gana da shugabannin Iran yayin ziyarar tasa, wadda ke zuwa a daidai lokacin da Tehran ke yin nazarin sababbin sharuddan Amurka na kawo karshen yakin na yankin Gabas ta Tsakiya.