Ba za mu bari a kafa kasar Falasdinu ba - Netanyahu
September 11, 2025
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa batun kafa kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci ba zai taba yiwu ba, a yayin wanin biki da ya jagoranta domin rattaba hannu kan shirin ci gaba da mamaye yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan.
A lokacin da yake wannan furuci mista Netanyahu ya nanata cewa Isra'ila za ta cika alkawarin da ta dauka na hana kafa kasar Falasdinu, tare da bayyana yankin na Gabar Yamma da Kogin Jordan a matsayin mallakin kasarsa.
Karin bayani: Abdallah II ya yi tir da mamaye Gabar Yamma da Kogin Jordan
A watan da ya shige ne dai Isra'ila ta amince da gudanar da wani gagarumin aiki na gina gidaje 3,400 a Gabar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, matakin da Majalisar Dinkin Duniya da wasu shugabannin kasashen duniya suka yi Allah wadai da shi.