Isra'ila ta ci gaba da kai farmaki a Gaza
October 4, 2025
Sama da mutane mutane 40 ne suka rasa rayukansu a hare-haren dakarun Isra'ila a Gaza, duk da sanarwar dakatar da farmakin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da ake ganin an kama hanyar kawo karshen yakin bayan fidda shawarwarin da ya ce dole Hamas ta amince da su kafin yammacin gobe Lahadi.
Wani jami'in Hamas ya ce a shirye suke da a fara tattaunawa a cikin gaggawa don cimma yarjejeniya.
Kazalika ya ce Masar, mai shiga tsakani a tattaunawar sulhu, za ta shirya wani taro don yanke shawara kan makomar Gaza bayan yakin.
Shawarar Trump ta bukaci a dakatar da yakin da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su cikin sa'o'i 72, da janyewar sojojin Isra'ila a hankali daga Gaza da kuma kwance damarar Hamas.
Karin Bayani: Trump ya nuna alamar samun maslaha a Gabas ta Tsakiya