Isra'ila ta kai wa babbar cibiyar makamashin Iran hari
April 6, 2026
A cikin wani sakon faifan bidiyo da ya wallafa, ministan tsaron Israel Katz, ya ce dakarunsu sun kai gagarumin hari kan babbar cibiyar sarrafa makamashin Iran ta South Parsa da ke Assalouyeh a ranar Litinin, wadda ya bayyana a matsayin muhimmiyar cibiya da ke sarrafa kusan rabin adadin albarkatun makamashi da Teheran ke tinkaho da su.
Iran na ci gaba da bijerawa shugaban Amurka Donald Trump
Kafofin yada Iran sun ruwaito cewa an jiyo fashe-fashen abubuwa da ba a bayyana adadinsu ba a wannan cibiyar hadin gwiwa tsakanin Iran da Qatar, wadda da ke kunshe da rijiyoyin iskar gas mafi girma a duniya.
EU ta yi tir da kai hare-hare kan ababen more rayuwa
Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Antonio Costa ya bayyana cewa ''duk wani hari kan ababen more rayuwa musamman ma cibiyoyin makamashi abu ne da ya saba wa doka kuma da ba za a amince da shi ba'', a daidai lokacin da aka shiga rana na 38 da barkewar yakin Iran da kawancen Amurka da Isra'ila.
Mista Costa ya kara da cewa al'ummar Iran su ne ke fama da matsalolin tsarin shugabancin kasarsu, kuma su ne za su fi kowa jin radadin wahala idan aka ci gaba da sara inda babu gaba, sai dai ba tare da ya ambaci sunan Amurka ko Isra'ila ba a sakon gargadin da ya ake yana mai bukatar a mayar da wukake cikin kube.
A baya-bayan shugaban majalisar Tarayyar Turan ya gana da shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian, inda ya bukaci Teheran da ta dakatar da kai wa kasashen yankin Gulf hare-hare, tare kuma da dawo da zirga-zirga a mashigar Hormuz. Hakazalika ya kuma jaddada cewa diflomasiyya ce hanya daya tilo domin warware wannan rikin na yankin Gabas ta Tsakiya.