1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila Ta Saki Jagoran Hamas Hassan Yousef Daga Gidan Yari

June 11, 2026

Isra'ila ta saki Hassan Yousef babban jagoran kungiyar Hamas a Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye, bayan tsare shi fiye da shekaru biyu ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba.

https://p.dw.com/p/5FEQl
Gidan yarin Isra'ila a garin Ramallah
Gidan yarin Isra'ila a garin RamallahHoto: Fanny Fascar/DW

Iyalansa ne suka tabbatar da hakan, inda dansa, Owais Yousef ya ce an saki mahaifinsa mai shekaru 71 a kusa da birnin Hebron kafin a kai shi asibiti a Ramallah, inda yake zaune.

Hassan Yousef na daga cikin wadanda suka kafa Hamas a shekarun 1980 tare da marigayi Sheikh Ahmad Yassin da wasu mambobin kungiyar Muslim Brotherhood ta Falasdinu.

An tsare shi ne tun watan Oktoban 2023 karkashin dokar tsare mutane ba tare da tuhuma ba, wadda Isra'ila ke amfani da ita musamman tun bayan barkewar yakin Gaza.

Isra'ila ta ce wannan tsarin na taimakawa wajen hana kai hare-hare yayin da ake ci gaba da tattara hujjoji, amma kungiyoyin kare hakkin bil'adama na zargin ana amfani da shi ba daidai ba.

Wannan ba shi ne karo na farko da aka tsare Hassan Yousef ba, domin an sha kama shi a lokuta daban-daban cikin shekaru da dama da suka gabata.