1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta yi luguden wuta a yankin Rafah na Gaza

October 19, 2025

Harin ya zo ne ana tsaka da aiwatar da yarjejeniyar tsagaitra wuta a Gaza wacce shugaban Amurka Donald Trump ya mika.

https://p.dw.com/p/52F6x
Wani gini da Isra'ila ta lalata a Gaza a yayin hare-haren da ta ke kaddamarwa
Wani gini da Isra'ila ta lalata a Gaza a yayin hare-haren da ta ke kaddamarwaHoto: Saeed M. M. T. Jaras/Anadolu/picture alliance

Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ta yi barin wuta a birnin Rafah da ke kudancin Gaza a ranar Lahadi, bayan dakarunta sun fuskanci harin ‘yan bindiga.

A wata sanarwa da rundunar sojojin kasar ta fitar ta ce "da safiyar yau, ‘yan ta'adda sun bude wuta kan dakarun IDF da ke gudanar da aikin lalata cibiyoyin ta'addanci a yankin Rafah bisa sharuddan yarjejeniyar tsagaita wuta.”

Isra'ila ta yi barazanar komawa filin daga

Sanarwar ta kara da cewa dakarun Isra'ilar sun mayar da martani da hare-haren jiragen yaki da kuma harbi da manyan bindigogi a yankin Rafah domin kawar da barazanar.

An lalata wasu ramukan karkashin kasa da gine-ginen soji da aka gano ana amfani da su wajen ayyukan ta'addanci a cewar sanarwar ta Isra'ilawa.

Shin za a iya raba Hamas da ikon Zirin Gaza?

Wannan harin ya zo ne ana tsaka da aiwatar da yarjejeniyar tsagaitra wuta a Gaza wacce shugaban Amurka Donald Trump ya mika.