Jamus ta kaddamar da makamun kare sararin samaniya
December 3, 2025
Kasar Jamus ta kaddamar da aiki da makamun kariya daga harin makamai masu linzami, wanda aka gina da zai iya cafke duk wani makamun da aka harba mai tafiya tsakanin kasa da kasa.
Dalilan karfafa tsaron Jamus
Haka yana cikin matakan da Jamus ke dauka tun bayan hare-haren da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine, tare da barazanar da Rasha ke yi ga sauran kasashen Turai.
Ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius ya jaddada cewa wanna kariya daga makamai masu linzami na cikin matakan kare kasar da ake dauka. Kuma wannan zai karfafa tsaro tsakanin kasashen kungiyar tsaron NATO.
Kasashe da dama na duniya suna muradin sayen wannan makamun kariya na Jamus, wanda Isra'ila ta yi amfani da shi lokacin da makamun ya taimaka wajen kare wasu hare-haren Iran lokacin fafatawa tsakanin kasashen biyu na Isra'ila da Iran.