Jamus za ta girka garkuwar sararin samaniya mai linzami
November 25, 2025
Rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr, ta sanar da gagarumin shirinta na kaddamar da garkuwar sararin samaniya mai linzami, ta Arrow 3 missile defence system, kirar isra'ila, a wani mataki na kara karfafa tsaron ko ta kwana.
Wata sanarwa da rundunar sojin samar kasar ta fitar, ta ce babban hafsan sojin Jamus Carsten Breuer da takwaransa na sojin sama Holger Neumann, su ne za su kaddamar da girka garkuwar, a ranar 3 ga watan Disamban 2025, a sansanin sojin sama na garin Holzdorf da ke Brandenburg.
Sanya wannan garkuwa, shiri ne da zai bai wa Jamus kariya daga ko wane irin makami mai linzami ko na roka, tare da lalata shi kai tsaye.
Karin bayani:Merz: Ko EU za ta raba gari da Isra'ila?
Wannan na zama shirin ko ta kwana daga barazanar hare-haren Rasha, wadda har yanzu ke ci gaba da mamayar makwabciyarta Ukraine sama da shekaru uku.