Rawar Afirka a gasar cin kofin duniya
June 12, 2026
Maroko dai tana daya daga cikin kungiyoyi mafi karfi a Afirka kuma tana cikin wadanda za a fafata da su a gasar cin kofin duniya ta 2026 da karfin gwiwa.
A wasannin neman cancantar shiga gasar, kungiyar ta mamaye rukunin E na Afirka, kuma ta lashe duk wasanni takwas, inda ta samu maki 24 mafi yawa, sannan aka ci ta kwallaye biyu kacal. Babban nasarar da ta samu ita ce a kan Jamhuriyar Kwango da ci 6 da nema. Wannan ya bai wa Maroko damar bayyana a karo na bakwai a gasar cin kofin duniya.
Rawar kasashen Afirka a baya
Bayan kifar da ita da wuri da dama a baya, kungiyar ta kafa tarihi a gasar cin kofin duniya ta 2022 ta hanyar zama kungiyar Afirka ta farko da ta kai wasan kusa da na karshe a gasar kuma daga karshe ta kare a matsayi na hudu.
Kazalika Maroko tana daya daga cikin kasashen Afirka mafi nasara a wannan fagen a nahiyar, bayan lashe gasar kofin kasashen Afirka sau biyu.
Jaridar ta Sportbild ta ci gaba da cewar, "Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na murnar dawowar ta zuwa matakin kwallon kafa na duniya a gasar cin kofin duniya ta 2026".
Kungiyar ta yi nasara a wasannin share fage masu mahimmanci da Kamaru, da Najeriya, da kuma Jamaica, wanda hakan ya tabbatar da matsayinta a gasar da yanzu aka fara fafatawa.
Ga Kwangon, wannan shi ne karo na biyu da ta buga gasar cin kofin duniya tun 1974, lokacin da kasar ta gabashin Afirka ke wasa da sunan Zaire. Da matasan 'yan wasa masu hazaka da karfin gwiwa, Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na da burin taka muhimmiyar rawa a wannan karon fiye da lokacin da ta fara gasar cin kofin duniya sama da shekaru 50 da suka gabata.
Sake dawowa bayan shekaru 12
Ita kuwa ta dawo dandalin gasar cin kofin duniya bayan shekaru 12, kuma ta yi fice a wasannin share fage na Afirka, musamman ma bangaren tsaron gida. An kasa doke su a wasanni 10, ba su yi asarar kwallo ko daya ba, kuma sun sami matsayi na farko a rukunin da suke kafin Gabon.
Nasarar da suka samu da jefa kwallo dai dai har tara 9 da nema a kan Seychelles ita ma wata alama ce ta nuna kwarewa da bajinta.
Wannan ya nuna bayyanar Cote d'Ivoire a karo na hudu a wasannin karshe na gasar cin kofin duniya. A wasanni uku da suka buga a baya, an cire kungiyar a matakin rukuni a kowane lokaci, amma a matsayinta na zakaran gasar cin kofin kasashen Afirka sau uku, tana cikin jerin kungiyoyin kwallon kafa mafi nasara a nahiyar.
Bayan nasarar da ta samu a gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2024, Cote d'Ivoire ta nufi gasar cin kofin duniya ta 2026 da sabon kwarin gwiwa.
Cutar Ebola
Daga batun wasanni sai kuma kokarin da ake yi na shjawo kan cutar Ebola da ke barazana a kasashen gabashin Afirka, inda jaridar Der Tagesspiegel ta wallafa labari mai taken "Idan Afirka ba ta da karfi, Turai za ta ji a jikinta"
Likitan Kwango kuma mai bincike Jean-Jacques Muyembe ya bayar da gagarumar gudummowa wajen gano cutar Ebola. Dangane da sake barkewar cutar, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar kusan mutane 600 zuwa yanzu, ya yi gargadin cewar har yanzu al'ummar duniya ba ta koyi darasi daga kurakuranta na baya ba.
Hukumomi a yankin gabashin Kwangon dai a yanzu haka sun dukufa wajen ilimantar da mutane don kare ta'azzarar yaduwarta.