1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ko Peter Obi zai zama shugaba?

Uwais Abubakar Idris LMJ
May 21, 2026

Jamiyyar adawa ta NDC ta tsayar da Peter Obi shi kadai a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben Najeriya da za a yi a watan Janairun shekara ta 2027 da ke tafe.

https://p.dw.com/p/5E4If
Najeriya | Peter Obi | Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso
Dan taakarar shugabancin Najeriya Peter Obi da Sanata Rabi'u Musa KwankwasoHoto: Nasiru Salisu Zango

Kwamitin tantance 'yan takara a NDC ne ya zartar da hakan, inda hakar Peter Obi  ta zama dan takarar neman shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jamiyyar ta cimma ruwa. Obi ya  zama dan siyasa na farko a Najeriyar da ya samu tabbacin zama dan takarar neman shugabancin kasar, a guguwar siyasar da ke kadawa yanzu.

Ko kawancen da Kwankwaso zai zama mafita?

Ya dai fice daga jamiyyar ADC ne ya ruga zuwa NDC, duk a kan wannan bukata ta samun takara. Mr Obi bai boye kwadayinsa ba, domin a lokuta da dama ya sha nanata cewa ba zai amince da matsayin mataimaki ga wanda za a ba takara a kowace jam'iyya ba. Wannan ya sanya shi kulla kawance da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimakinsa.

DW ta tattauna da Dakta Yunusa Tanko

Tuni ya kaddamar da taken yakin neman zabe na OK maimakon Obedient da ya yi amfani da shi a baya. Samun nasarar Obi ta zama dan takarar neman shugaban kasa a Najeriya, ya sauya lissafin zaben kasar musamman ga shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu. Obi dai na da goyon baya a yankin Kudu maso Gabashin Najeriyar, abin da zai shafi kuru'un da shugaban kasar mai ci da jam'iyyarsa ta APC ke hasashen samu.

Rashin tabbas ga jam'iyyun adawa

Ya sha yawace-yawace a jam'iyyun siyasar Najeriyar, kama daga PDP ya zuwa Labour da ADC a yanzu kuma ya ci birki a NDC tare da kulla kawance da jagoran Kwankwasiya. Har zuwa yanzu dai akwai rashin tabbas a kan yadda jam'iyyuna adawar Najeriyar za su tunkari zaben kasar na 2027, saboda rarrabuwar kawuna.

 

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani