Kremlin ta amince da tsagaita bude wuta a Ukraine
January 31, 2026
Talla
Sai dai Kremlin ta ce duk da Rasha ta amince da wannan bukata, amma za ta dakatar da kai hare-harenta ta sama a Kyiv har zuwa ranar 1 ga Fabrairu ne kawai.
Tun da farko shugaban kasar Volodymyr Zelenskyy ya ce Ukraine za ta daina kai hare-hare kan Rasha idan Rasha ta dakatar da kai hare-hare kan kayayyakin makamashin Ukraine.
Zelensky ya ce shawarar tsagaita bude wuta ta fito ne daga Washington.
Shugaban Ukraine ya kuma ce masu shiga tsakani sun kasa cimma matsaya kan iko da yankin Donetsk dake gabashin Ukraine. Wanda Rasha ke neman Ukraine ta mika yankin da ya jima karkashin ikon ta.
Ana sa ran ci gaba da tattaunawa atsakanin bangarorin biyu da kuma masu shiga tsakani a birnin Abu Dhabi na kasar hadaddiyar Daular Larabawa.