Tattaunawar kawo karshen yakin Ukraine a Abu Dhabi
January 25, 2026
Shugaba Zelenskyy ya ce an tattauna a kan abubuwa da dama a zaman sulhu a birnin Abu Dhabi, sai dai an fi mayar da hankali kan matakan kawo karshen yakin na Ukraine.
Wakilan da suka halarci zaman tattaunawar ana sa ran su mika rahoto ga gwamnatocinsu domin ganin matakai na gaba da za a dauka. Zelenskyy ya ce za a gudanar da wasu tarurruka a farkon makon gobe. Wani mai magana da yawun gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce tattaunawar ta fitar da batutuwa na kai tsaye a daftarin shirin zaman lafiya da Amurka ta gabatar.
Karin bayani: Saura kiris Ukraine ta samu zaman lafiya - Trump
Kawo yanzu babu wani cikakken bayani kan abin da aka tattauna, sai dai rahotannin a baya sun yi nuni da cewa, batun ikon mallakar yankuna aka fi mayar da hankali a kai. Rasha ta matsa lamba sai Ukraine ta janye dakarunta daga yankunan gabashin Dombas da Moscow ba ta da iko da shi, sai dai Kyiv ta ki amincewa da wadannan bukatun.