Macky Sall ya dage kan neman mukamin Sakataren MDD
March 28, 2026
Tsohon shugaban kasar Senegal Macky Sall ya bayyana cewa yana kan bakansa domin tsayawa takarar numan mukamin babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya domin maye gurbin Antonio Guterres, duk da matakin Kungiyar Tarayyar Afirka na kin goyon bayan takararsa.
Kimanin kasashe 20 ne dai na kungiyar Tarayyar Afirka wadanda ba a bayyana sunayensu ba suka nuna adawa da takarar Makcy Sall, wanda ya jagoranci kasar Senegal daga shekarar 2012 zuwa 2024.
Daga cikin kasashen da suka ki marawa takarar Sall har da kasarsa Senegal, inda shugabanni masu ci ke zargin sa da yunkurin murdewa dimokuradiyya wuya a rikicin siyasar da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a tsakanin 2021 zuwa 2024, tare da kuma da boye muhimman bayanan tattalin arziki musamman ma bashin da ake bin kasar.
Senegal ta karyata sake cin bashi a asirce
A tsarin shiga takarar neman kujerar sakataren Majalisar Dinkin Duniya dai dole ne kowanne dan takara sai ya samu sahalewa daga wata kasa ko kungiyar kasashe, amma ba lallai sai kasarsa ta asali ba.