'Yan sandan jiha zasu magance rashin tsaro?
June 11, 2026
'Yan majalisar sun tsara yadda 'yan sandan zasu yi aiki tare da na gwamnatin tarayyar kasar, ko wane tsari suka yi don kaucewa tsoton gwanonin jihohi su yi amafani da su da ma batun sanya kabilanci a lamarin?
Bayan kwashe tsawon shekaru ana muhawara, matsin lamba da ma jan kafa ne ‘yan majalisar wakilan Najeriyar suka amince da kafa 'yan sandan jihohi a matakin da suka bayyana da kokari ne na shawo kan matsalar rashin tsaro. Gyaran fuska suka yi wa sassa na 84, 214 da 214 na tsarin mulkin Najeriyar wanda cikin kankanin lokaci suka jefa kuri'a tare da amince da shi. Bisa gyaran da suka yi za'a samu 'yan sandan jihohi da na tarayya wadanda zasu ci gaba da aiki a jihohi. Hon Makki Abubakar Elleman ya shaida min abinda suka hango ya sanya su amincewa da dokar.
Karin bayani: Ko sababbin matakan tsaro za su ceci Najeriya?
Garambawul ne suka yiwa dokar aikin yan sanda ta Najeriyar domin an samawa yan sandan jihohin yanci tare da hana katsalandan daga yan sandan tarayya in dai ba an samu matsalar rashin bin doka daga ‘yan siyasa ba ne. Duk da wannan gyara da suka yi sai ya samu amincewar majalisun dokokin na jihohi abinda ya sanya nuna damuwa sanin halin da jihohin ke ciki na kokke basu da kudi. Amma Hon Bello Shinkafi ya ce suna da karfin guiwar jihohin zasu yi abinda ya dace.
Amincewa da kudurin doar da majalisar wakilai ta yi wani muhimmin sauye-sauye ne da aka dade ana has ashen faruwarsa tun 1999 da Najeriyar ta koma mulkin farar hula. Kungiyoyin kare hakkin jama'a sun yi kashedin sanya idanu don yin abinda ya dace.
Amma wane shiri 'yan majalisar suka yi don kaucewa gwamnonin jihohi su yi amfani da 'yan sanda don biyan bukatun kansu?
Karin bayani: 'Yan bindiga sun sace dalibai a Zamfara
'Yan majalisar dattawan Najeriya ma sun tattauna a kan wannan batu inda suka tura shi ga ga kwamitin gyaran fuska ga tsarin mulki muhawa a kan wannan batu da ke daukan hankali sosai. Idan an samu nasara kafa yan sandan jihohiNajeriya zata shiga sabon babi na samun jami'an tsaro da zasu iya taimaka shawo kan matsalolin tsaro musamman na garkuwa da jama'a.