Zanga-zangar masu fafutuka sauyin yanayi a taron COP30
November 16, 2025
Talla
Taron gangamin, wanda masu shirya shi suka yi wa lakabi da "Tattakin Al'umma", ya zo ne bayan zanga-zangar da 'yan asalin kasar Brazil suka gudanar a farkon makon bude taron.
A ranar Asabar, masu zanga-zangar sun yi tattaki mai nisan kilomita hudu da rabi sanye da bakaken kaya, don nuna damuwa a kan yadda hayaki dake gurbata muhalli.
Masu zanga-zangar sun jera akwatunan da ake daukar gawa guda uku dauke da kalaman "kwal" da "man fetur " da "gas."
Taron na COP30 a Belem wanda za a kammala shi a karshen mako, masu fafutukar kare muhallin na fatan za a samu ci gaba kan matakan da ake dauka don magance matsalar sauyin yanayi da illolinsa.
Karin Bayani: COP30: Ko kasashen duniya za su hada kai?