SiyasaIsra'ila
JD Vance na yin ziyara a Isra'ila
October 21, 2025
Talla
JD vance wanda ya kai ziyara a Israi'la da nunfin karfafa shirin tsagaita wutar, ya ce ba za su giciya wa'adi ba na ganin Hamas ta kwance damara mayakanta amma dai ta gaggauta yin haka.
Amurka da Isra'ila sun zargi Hamas, da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza, inda aka yi mummunar tashe-tashen hankula a ranar Lahadin da ta gabata wadanda suka yi barzana ga shirin zaman lafiyar.
Wannan tsagaita wutar da ya fara aiki a ranar 10 ga watan Oktoba, shi ne, na uku bayan shafe shekaru biyu ana yaki a Gaza,
sakamakon harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba, na shekara ta 2023 wanda ba a taba ganin irinsa ba.