Gangamin adawa da Trump ya barke a biranen Amurka
October 18, 2025
An kaddamar da gamgamin adawa da Donald Trump a sassa daban-daban na Amurka a Asabar din nan, kama daga birnin New York zuwa San Francisco, gangamin da magoya bayan shugaban suka bayyana a matsayin kiyayya ga Amurka.
Wadanda suka shirya gangamin da aka yi wa lakabi da 'No Kings' sun ce ana sa ran miliyoyin Amurkawa za su yi tattaki domin yin Allah wadai da karfin iko da shugaba Trump ke nunawa tun bayan dawowarsa kan madafun iko.
Fiye da taruka 2,700 ne ake shirin gudanarwa a wannan rana ta Asabar a manya da kananan birane na fadin Amurka, ciki kuwa har da kusa da gidan da Donald Trump ke hutun karshen mako wanda ke a jihar Florida.
Karin bayani: Baki miliyan daya sun fice daga Amurka saboda Trump
Wannan rana ta gangami dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurka ta gaza samar da kasafin kudi, yayin kuma da Donald Trump ya tura sojoji zuwa jihohin da ke karkashin gwamnonin jami'ayyar Democrat domin yaki da bakin haure da kuma masu aikata muggan laifuka.