1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Muna daf da amincewa a kafa kasar Falasdinu — Japan

Abdoulaye Mamane Amadou Muntaqa Ahiwa
September 24, 2025

Shugaban gwamnatin Japan ya bayyana cewa kasarsa a shirye take da amincewa da kafa kasar Falasdinu mai cikakken 'yancin kai don samar da zaman lafiya

https://p.dw.com/p/50yyu
USA New York | Firaministan Japan Shigeru Ishiba
USA New York | Firaministan Japan Shigeru Ishiba Hoto: Eduardo Munoz/REUTERS

Kasar Japan ta ce yarda da amincewa da kafa kasar Falasdinu a matsayin kasa mai cikakken 'yancin kanta batu ne na dan lokaci kawai.

Shugabannin duniya sun fara jawabi a taron MDD na 80

 A cikin jawabinsa na zauren taron Majalisar Dinkin Duniya, firaministan Japan Shigeru Ishiba, ya bayyana damuwa karara kan kalaman shugaban gwamnatin Isra'ila na yin kememe da batun kafa kasar Falesdinu, inda har ma da bayyana anniyarsa ta ci gaba da mamaye gabar yamma ga kogin Jodan.

Shigeru Ishiba ya ce "Batun ba wai na amincewa da kasar Falasdinu kadai mai cikakken 'yancin kai ba ne, amma har a yaushe, domin abubuwan da gwamnatin Isra'ila ke aikatawa a yankin abun Allah wadai ne."

Jamus na cikin ruɗani a kan amincewa da Falasdinu

A cewar wata kididdigar, kasashe 150 ne daga cikin 193 a yanzu suka amince da kafuwar kasar Falasdinu, ciki har da Burtaniya da Faransa da Kanada, to amma kuma a daidai lokaci guda ita kuwa Amurka ta yi fatali da shirin.