1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Takaddamar 'yan takara a Jam'iyyar APC

May 18, 2026

A yayin da ake shiga zagaye na biyu na kokarin fidda gwanayen jam'iyyar APC tsoro da kila faduwar gaba daga dukkan alamu sun mamaye masu tsintsiyar tarayyar Najeriyar

https://p.dw.com/p/5DvYl
Zaben fidda Gwani na Jam'iyyar APC a Najeriya
Hoto: SAMUEL ALABI/AFP

An dai share kusan karshen makon jiya cikin rudanin fidda gwanayen APC a majalisar wakilai ta kasar. Kama daga Yobe ya zuwa Edo da ma jihar Plateau ko bayan Katsina dai Jiga jigan yan APC kusan 26 ne suka yi asarar damar sake komawa zauren majalisar wakilan a wani abun da ke daukar hankali da kila aika tsoro cikin gidan tsintsiyar.

To sai dai kuma fidda gwanayen APC ya kare a jihohin kasar da dama. Da yawa an rufe kofa ga sabbabin masu takara cikin jam'iyyar, bisa umarnin fadar gwamnatin kasar na ramuwar biki bisa goyon bayan wakilai ga shugaba Bola Tinubu.

Zaben fidda wani na APC na cike da rikici

Zaben fidda gwani na Jam'iyyar APC
Hoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Kaso 85 cikin dari na gwanayen dai na zaman tsofaffin da suka nuna goyon baya bisa manufofin shugaban kasar a shekaru uku na mulkinsa. Abun kuma da ke nuna alamun dawowa daga rakiyar demokaradiyya ta gida ya zuwa Fifita abokan burmi.

Karan tsaye ckin tsari babba, ko kuma kokarin cikon alkawari. Ana dai kallon sabon matakin da ya rufe kofa ga daruruwan sabbabin yan APC na iya jawo illa cikin gidan jam'iyyar.

Duk da cewar dai dokar zabe ta haramta sauyin sheka bayan kamalla zabukan fidda gwanayen, akwai tsoron zagon kasa cikin gidan APC.

Su waye za su samu takarar APC a Najeriya?

Zaben fidda gwani na Jam'iyyar APC
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Baya can cikin tarihi dai zagon kasan ya kai ga kirga asara a bangaren PDP da ta share shekaru dai dai har 16 tana fada ana amsawa.

To sai dai kuma duk dan da ke zaman na halali to yana zama wajibi ya yi biyayya ga ubansa, a tunanin Yusuf Dingyadi da ke baiwa shugaban jam'iyyar shawara a harkar labarai.

A kusan daukacin jihohin kasar dai zabin gwamnoni dama ragowar jiga jigan jam'iyyar ne aka bayyana da samun nasara cikin batun fidda gwanayen.

An kuma haramtawa yan kwamitocin yin zaben hira da kafafen labarai a wani yunkuri na kauce wa baki biyu cikin gidan tsintsiyar.