1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tinubu na nema a yi sulhu a APC

May 15, 2026

wani abun dake nuna alamu na damuwa cikin gidan APC mai mulki, shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu ya yi gargadin fuskantar matsala cikin gidan jam'iyyar in har ba'a kai ga samun daidaito ba.

https://p.dw.com/p/5Doon
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed TinubuHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Dab da fara fidda gwanayen  APC, cikin wata wasikar da ke zaman irin ta ta farko dai  Tinubun ya ce 'yan  APC na da bukatar neman hanyar sulhu da kaucewa rikciin da ke iya daukar hankali cikin gidan na adawa.

A cikin rashi na tabbaci ne dai miliyoyin 'yayan jam'iyyar APC ke shirin fara zabukan fidda gwani a mazabun kasar sama da dubu takwas a tarayyar Najeriya.

An dai share kusan makonni guda  biyu ana dogon turanci a tsakanin 'yayan jam'iyyar bisa kokari na sulhunta tsakanin da ya rikide ya zuwa dauki a dora a matakai daban daban cikin jam'iyyar.

Kafin kai wa ya zuwa fidda gwanayen da ake yi wa kallon zakaran gwajin dafi bisa makomar jam'iyyar da kila  cigaban dorewar tsintsiyar a madaurinta daya.

Magoya bayan jam'iyyar APC
Magoya bayan jam'iyyar APCHoto: SAMUEL ALABI/AFP

A yau ne dai aka tsara fara fidda  gwanayen 'yan majalisar ta wakilai, kafin rashin na tabbaci ya kai a dage shi ya zuwa  Asabar.

Bala Ibrahim dai na zaman darakatan labaran jam'iyyar da kuma ya ce kokari na kaiwa zuwa zama na lafiya da ingantar tsari ne  ya kai ga dage taron mai tasiri.

Duk da cewar dai suhun ta nemi gagara a jihohi dabam dabam, akwai kuma tsoron kato bayan katon na iya kara yamutsa lamura cikin gidan APC da ke da burin kaucewa tsautsayi.

Rashin na tabbacin ne  dai daga a dukka na alamu ya dauki hankali na shugaba Bola Tinubu da ya aike da wata wasika da yake jan kunnen ya'yan APC da su kaucewa tsautsayi.

Magoya bayan jam'iyyar APC
Magoya bayan jam'iyyar APCHoto: Ubale Musa/DW

Tinubun da ya ce masu adawar kasar sun zura ido  da nufin neman ganin gazawar ta tsintsiya dai ya baiyana goyon bayan sulhu cikin dabarar samar da gwanayen, kafin kaiwa y azuwa  yar kwanji in ta kama.

To sai dai kuma daga dukka na alamu miliyoyin 'ya'yan APC ba sa da niyyar sauraro na shugaban a cikin neman cika buri.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani