1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ya ake ciki a siyasar jihar Bauchi?

Aliyu Muhammad Waziri LMJ
May 14, 2026

Yayin da jam'iyyu ke ci gaba da shirin tunkarar zaben 2027, a jihar Bauchi jam'iyya mai mulki ta APM ta kammala nata zaben fitar da gwanin ta hanyar samun daidaito a tsakanin 'yan takara a kujeru dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/5Dlm1
Najeriya | Bauchi | Siyasa | Gwamna | Bala Mohammed
Gwamnan jihar Bauchi a Najeriya Dakta Bala MohammedHoto: Ubale Musa/DW

Wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 47 da aka samu dan takara daga shiyyar Katagum wanda ya fito daga jam'iyya mai ci, tun bayan marigayi Alhaji Tatari Ali a shekara ta 1979 a jamhuriya ta biyu. A yanzu, Dakta Yakubu Adamu tsohon kwamishinan kudi na jihar Bauchi da kuma ya kasance dan karamar hukumar Giade da ke shiyyar ta Katagum ne shi ne dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar APM mai mulki.

Wa zai zama gwamna a Bauchi?

Kafin tsaida shi a matsayin dan takara ta hanyar daidaito, Honourable Faruq Mustapha da shi ma ya fito daga shiyyar ta Katagum yna daga cikin na sahun gaba wajen samun takarar. Siyasar jihar Bauchi tana da fuskoki biyu wadanda suka hada da ta cikin gari da kuma wacce ta karade jihar baki daya.

Hira da gwannan jihar Bauchi Bala Mohammed

Sau tari al'ummar cikin gari ba su cika goyon bayan wanda ya fito a bangaren jam'iyyar gwamnati ba, saboda a nan adawa ta fi karfi duk da cewa kuma nasarar lashe zaben ta ta'allaka ne a daga wajen gari. Masu sharhi kan al'amuran siyasa a jihar kamar Dakta Ibrahim Adamu na mai bayyana cewa, takarar jam'iyyar ta APM na cikin siradi.

Wa APC za ta tsayar takarar gwamna?

Tun ba yanzu ba, matasa ke korafin ana barinsu a baya wajen ba su damar tsayawa takara a manyan kujeru kamar ta gwamna, shi ya sa a wannan karon masu jini a jikan suka ce suna tare da Dakta Yakubu Adamu.Yanzu hankali ya karkata ne zuwa ga jam'iyyar APC wacce ke da manyan masu neman takara da suka hadar da tsohon gwamna M.A Abubakar da Dakta Bala Wunti da Sanata Shehu Buba Umar. Za a gudanar da zaben fitar da gwani a APC a ranar 21 ga wata na Mayun 2026, domin sanin wanda zai rike mata tutar takarar gwamnan.

Gyarawa da wallafaawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani