Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin kashe fararen hula
May 12, 2026
Kungiyar Amnesty International dai a wata sanarwa da ta fitar ta ce dakarun sojin Najeriya sun halaka fararen hula akalla 100 a wata kasuwa da ke yankin Tumfa a jihar Zamfara. Kazalika wani jami'in kungiyar Red Cross a jihar, Ibrahim Bello Garba, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na AP mutuwar mutane 80 a kauye guda.
Karin bayani: Sojin Najeriya sun musanta zargin kashe jama'a a jihar Niger
Daraktan kungiyar Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce galibin wadanda aka halaka 'yan mata ne da kuma kananan yara.
Karin bayani:Sojojin Najeriya sun yi ikrarin kashe mayan ISWAP 50
Mai magana da yawun sojojin Najeriya Manjo Janar Michael Onoja, ya musanta zargin halaka fararen hulan, inda ya ce sun kaddamar da farmakin ne kan 'yan ta'adda a yankin kuma suna ci gaba da samun galaba a kokarinsu na murkushe 'yan bindiga. Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na zargin rashin samun cikakken bayanan sirri na kai hari tsakanin sojojin saman Najeriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama bisa kuskure.