Sojin Najeriya sun musanta zargin kashe jama'a a jihar Niger
May 11, 2026
Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton da ke zarginta da halaka dimbin jama'a, a harin da ta kai jihar Niger da ke tsakiyar kasar a karshen mako, wanda ta ce 'yan bindiga 70 ta halaka, amma tana jajantawa iyalan mutane 13 fararen hula da harin ya ritsa da su bisa kuskure.
Karin bayani:Harin ta'addanci a arewacin Najeriya ya halaka mutane 45
Shelkwatar tsaro ta Najeriya, cikin wata sanarwa da ta fitar, mai dauke da sa hannun kakakinta Manjo Janar Michael Onoja, ta ce ta kai hare-hare maboyar 'yan bindiga a kauyukan Katerma da Bokko da Kusasu da kuma Kuduru, a jihar ta Niger, wanda ya kashe 'yan ta'adda 70.
karin bayani: Zamfara: Zanga-zangar mata kan tabarbarewar tsaro
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, ya raiwato shugaban karamar hukumar Shiroro Isyaku Bawa, na cewa harin sojojin na Najeriya ya kashe fararen hula 13 ranar Lahadi.
Karin bayani: Sojojin Najeriya sun yi ikrarin kashe mayan ISWAP 50
Ko a watan Afirilun da ya gabata ma, wani harin sojin Najeriya ya kashe mutane 56, a kasuwar Jilli da ke kan iyakar jihohin Yobe da Borno, a yankin arewa maso gabashin kasar, wanda mahukuntan kasar suka kaddamar da binciken gano ainihin mutane da aka kashe, fararen hula ne ko 'yan ta'adda, amma har yanzu babu karin bayani game da sakamakon binciken.
karin bayani:Attajirin Afirka Aliko Dangote zai gina matatar mai a Kenya
A wani labari kuma harin 'yan bindiga a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya, ya halaka mutane 30, in ji wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, ya ce maharan sun yi wa mamatan kwanton bauna a lokacin da suke tsaka da tafiya, cikin daren Lahadi.
Karin bayaniMutane 166 da aka sace a Kadunan Najeriya sun kubuta
Matafiyan da suka rasa rayukansu sun hada da fararen hula da mafarauta da kuma 'yan sa kai, da ke bai wa al'umma kariya daga 'yan bindiga.