NATO ta kakkabo jiragen yakin Rasha a samaniyar Estonia
September 20, 2025
Kungiyar tsaro ta NATO ta sanar da cewa ta kakkabo wasu jiragen yakin Rasha guda uku sumfurin MiG-31 da suka kutsa sararin samaniyar kasar Estonia ba tare da izini ba, lamarin da kasashen Turai suka bayyana a matsayin ganganci.
Firaministan Estonia Kristen Michal, ya ce kasarsa ba za ta laminci wannan lamari ba, sannan ya bukaci NATO ta aiwatar da ayar doka mai lamba hudu ta kundin yarjejeniyar kafa kungiyar wadda ta tanadi gudanar da taron gaggawa idan wani memba ya fuskantar barazana.
Karin bayani: Atisayen Rasha da Belarus ya tayar da hankali kasashen Yamma
Hakazalika jami'ar diflomasiyyar EU Kaja Kalas, ta tir da keta sararin samaniyar kasashen Tarayyar Turai a karo na uku, yayin da sakataren NATO Mark Rutte ya yaba da martanin gaggawa da dakarun kungiyar suka yi na kakkabo jiragen yakin na Rasha.
Sai dai a cikin wata sanarwa ma'aikatar tsaro ta Rasha ta yi watsi da wannan zargi da ke shirin bude sabon babin tankiya a tsakanin Moscow da kungiyar tsaro ta NATO.