SiyasaAfirka
Rasha ta alkawarin daina saka 'yan Kenya aikin soja
March 16, 2026
Talla
Ministan harkokin wajen kasar Kenya, Musalia Mudavadi ya bayyana cewa kasar Rasha ta yi alkawarin daina saka 'yan Kenya aikin soja domin karawa a yakin da ke faruwa tsakanin kasashen na Rasha da Ukraine.
Abin da aka tattauna
Mudavadi ya shaida haka lokacin taron manema labarai a birnin Moscow na Rasha, inda yake ziyara bayan ganawa da Sergei Lavrov ministan harkokin wajen kasar ta Rasha.
Hukumomin tsaron Kenya sun yi kiyasin cewa akwai fiye da 'yan kasar ta Kenya 1,000 suke fagen-daga a wannan yaki tsakanin Rasha da Ukraine. Sannan Kenya ta kulla yarjejeniyar ganin 'yan kasar sun kara samun damar aiki a kasar ta Rasha.