SiyasaTurai
EU: Karshen dangantaka da Amurka ya zo?
January 20, 2026
Talla
Ursula von der Leyen ta ce barazanar da Shugaba Donald Trump ke kara yi, ba za ta haifar da komai ba sai dai bai wa makiya dama da kuma dakile kokarin da suke na yakar abubuwan da ke yin barazana ga zaman lafiya. A cewarta, za su mayar da martani ba tare da fargaba ba kuma cikin hadin kai. Shugabar Hukumar Gudanarwa ta Kungiyar Tarayyar Turan ta bayayana hakan ne a jawabin da ta gabatar yayin taron tattalin arziki da ke gudana a birnin Davos na kasar Switzerland, inda ta ce: "Abin da nake so na bayyana shi ne, idan wannan sauyin ya kasance na din-din-din, to tilas Turai ma ta sauya na din-din-din. Lokaci ne da za mu yi amfani da wannan dama, mu samar da sabuwar Turai mai 'yanci."