SiyasaAfirka
Shugaban Masar ya sauya ministan tsaron
February 11, 2026
Talla
A wannan Laraba an nada Janar Ashraf Salem Mansour a matsayin sabon ministan tsaron kasar Masar. Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya rantsar da sabon ministan tare da wasu ministocin cikin wani takaitaccen sauyi da aka samu a majalisar zartaswar kasar. Shugaban ya yi alkawarin ci gaba da aikin bunkasa tattalin arzikin kasar.
Shi dai Janar Mansour ya maye gurbin Janar Abdel Majeed Saqr, wanda yake rike da mikamun na ministan tsaron tun watan Yuli na shekara ta 2024.
Tuni dai majalisar dokokin kasar ta Masar ta amince da matakin sauyin da aka samu a ma'aikatar tsaron kasar.