1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sauyin yanayi na daukan hankali

Suleiman Babayo ATB
November 11, 2025

Wakilai daga kasashen duniya suna ci gaba da muhawara yayin da aka shiga rana ta biyu kan taron sauyin yanayi na duniya da Brazil ke daukan nauyi.

https://p.dw.com/p/53R9X
'yan gwagwarmaya ke nuna irin matsalolin sauyin yanayi a wajen taro a Brazil
'yan gwagwarmaya ke nuna irin matsalolin sauyin yanayi a wajen taro a BrazilHoto: Igor Mota/ZUMA/picture alliance

Duk da gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump ba ta tura wakilai zauren taron Majalisar Dinkin Duniya kan kare muhalli ba, amma an samu gwamnonin jihohin California da New Mexico daga kasar ta Amurka wadanda suke cikin mahalarta taron, kuma suna cikin jihohin kasar ta Amurka masu karfin tattalin arziki. Akwai fata mahalarta taro su cimma manufofin da za su taimaka wajen magance matsalolin na sauyin yanayi a duniya.

Burin taron

'yan gwagwarmaya ke nuna irin matsalolin sauyin yanayi a wajen taro a Brazil
'yan gwagwarmaya ke nuna irin matsalolin sauyin yanayi a wajen taro a BrazilHoto: Allison Sales/dpa/picture alliance

Taron da ke gudana a birnin Belem na kasar Brazil na neman magance matsalolin sauyin yanayi bisa matakan hadin kai tsakanin kasashen domin dakile matsalolin gurbatar muhallin dan Adam.

Kana ana tantance yuwuwar bai wa kasar Habasha daga nahiyar Afirka damar daukan nauyin taron na shekara ta 2027, yayin da ake takaddama kan kasar da za ta dauki nauyin taron na shekara mai zuwa ta 2026 tsakanin kasashen Australiya da Turkiyya.