1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump: An kusa daina yakin Rasha da Ukraine

December 16, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ana samun ci-gaba a tattaunawar da ake yi domin kawo karshen yakin da Rasha ke yi da Ukraine.

https://p.dw.com/p/55Pvq
Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Andrew Caballero-Reynolds/AFP/Getty Images

Da yake magana a Washington a ranar Litinin, Trump ya bayyana cewa tattaunawar ta kai wani mataki na ci-gaba da ba a taba kaiwa  a baya ba. Ya ce ya tattauna da shugabannin kasashen Turai, ciki har da Jamus tare da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, inda ya kara da cewa duk da alamun ci-gaba, lamarin yana da sarkakiya.Trump ya kuma nuna cewa Amurka ta riga ta yi tattaunawa a lokuta masu yawa da Rasha kan hanyoyin warware rikicin.

Karin bayani: An gudanar da tarruka a asirce a kan Ukraine tsakanin Amurka da Rasha

A ranar Litinin wakilan Ukraine da Amurka sun gana a birnin Berlin na Jamus domin tattauna wani shirin samar da zaman lafiya mai kunshe da manyan batutuwa 20 da ya kamata Rasha da Ukraine su amince da su kafin kaiwa ga tsagaita wuta ta din-din. Tawagar Amurka na kunshe da wakilin musamman Steve Witkoff da kuma surukin Trump, Jared Kushner. Rasha ba ta halarci wadannan tattaunawa ba.