1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Tsohon shugaban Philippines na fatan tsallake shari'ar ICC

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 31, 2025

Rodrigo Duterte na fuskantar zargin halaka dubban mutane a yakin da ya ce yana yi da masu safarar muggan kwayoyi.

https://p.dw.com/p/4sUSy
Hotunan wasu da aka kashe lokacin mulkin Rodrigo Dutert a Philippines
Hoto: Basilio Sepe/ZUMAPRESS.com/picture alliance

Lauyan tsohon shugaban Philippines Rodrigo Duterte ya bayyana cewa akwai kwararan hujjojin da suke da su da za su sanya kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC yin watsi da tuhumar kisan kiyashin da ake masa, tun ma gabanin fara yi masa shari'a.

Karin bayani:Tsohon shugaban Philippines Duterte ya shiga komar yan sanda

A tattaunawarsa da manema labarai a birnin The Hague ranar Lahadi, Mr Nicholas Kaufman ya ce ficewar da Philippines ta yi daga cikin kasashen duniya da suka amince da kotun tun kafin fara tuhumarsa da aikata laifin ta gamsar cewa ba ta da hurumin tuhumarsa ballanta yi ma sa shari'a.

Karin bayani:Duterte ya isa kasar Netherlands don fuskantar shari'a a ICC

Rodrigo Duterte na fuskantar zargin halaka dubban mutane a yakin da ya ce yana yi da masu safarar muggan kwayoyi lokacin yana shugabancin Philippines.