1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine ta yaba tattaunawa da ta yi da Rasha a Abu Dhabi

Mouhamadou Awal Balarabe
February 4, 2026

A cikin sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta bayan kammala tattaunawa a ranar farko, wakilin Ukraine Rustem Umerov ya danganta ta da mai ma'ana saboda an mayar da hankali kan matakai na zahiri.

https://p.dw.com/p/585Uw
Wakilan Amurka da Rasha da Ukraine nsun hadu a Abu Dhabi don neman mafita ga yaki
Wakilan Amurka da Rasha da Ukraine nsun hadu a Abu Dhabi don neman mafita ga yakiHoto: UAE Government/REUTERS

Ukraine ta nunar da cewa tattaunawa da ta yi da wakilan Rasha da Amurka a Abu Dhabi don neman mafita ga yakin shekaru hudu ta kasance mai matikar ma'ana da amfani. A cikin sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta bayan kammala tattaunawar a ranar farko, babban mai shiga tsakani na Ukraine Rustem Umerov ya ce "aikin ya mayar da hankali kan matakai na zahiri da mafita masu amfani," inda ya ci gaba da cewar za a dora inda aka tsaya a ranar Alhamis.

Karain bayani: Shawari 28 na sasanta Ukraine da Rasha

Kasar Rasha na ci gaba da matsa wa Ukraine lamba, inda ta yi barazanar ci gaba da kai mata hare-hare mataikar fadar mulki ta Kyiv ba ta amince da sharuddan da ta gidanya mata ba. A kwanakin baya dai, Rasha ta bayyana cewar daya daga cikin sharudanta "masu mahimmanci" shi ne janye dakarun Ukraine daga yankunan da har yanzu take iko da su a yankin Donbas na gabashin kasar.

Karin bayani: Kokarin Turai na kawo karshen yakin Ukraine

Tattaunawar diflomasiyya da ake yi akai-akai tsakanin bangarorin biyu sun gaza kawo karshen rikici mafi muni a Turai tun bayan yakin duniya na biyu, wanda ya fara lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine a watan Fabrairun 2022.