Wakilan Isra'ila da Hamas zasu yi ganawar keke da keke
October 5, 2025
Masar dai ta gayyaci wakilan Isra'ila da na kungiyar Hamas tattaunawa domin tsara jadawalin musayar fursunoni yaki tsakanin bangarorin biyu, bayan daftarin wanzar da zaman lafiya da tsagaita bude wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar.
Karin bayani: Qatar da Masar na jiran ra'ayin Isra'ila kan yakin Gaza
Kafofin yada labaran Masar sun rawaito cewa ana sa ran gudanar da taron a birnin al-Arish da ke gabar Tsibirin Sinai da Sharm El-Sheikh na kusa da yankin Zirin Gaza. Ana sa ran Manzon Amurka na Musamman a yankin Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff zai halarci taron.
Karin bayani:An gaza sasanta Isra'ila da Hamas a Qatar
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yana da yakinin cewa nan bada jimawa ba za a saki dukkan fursunonin yakin kasar da ke hannun kungiyar Hamas a yankin Gaza, wanda kuma hakan babbar nasara ce ga hukumomin Tel Aviv.