Yaki da Iran ya ci mana dala biliyan 25 - Amurka
April 29, 2026
Babban jami’in kuɗi na Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon ya bayyana cewa kawo yanzu Amurka ta kashe zunzurutun kudi dala biliyan 25 a yaki da Iran.
Wannan dai shi ne bayani da ‘yan Democrat suka dade suna nema musamman daga wajen ma'aikatar.
Amurka ta sake kama jirgin dakon man Iran a tekun Indiya
Shi kuma Sakataren Tsaron Amurkar, Pete Hegseth, ya bayyana cewa ‘yan jam'iyyar Democrat a majalisar su ne "manyan abokan gaban da kasar ke fuskanta.
Hegseth ya fadi haka ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan majalisa a ranar Laraba karo na farko tun bayan da Donald Trump ya fara yaƙi da Iran.
Amurka ta fitar da jerin sunayen dakarunta da Iran ta halaka
Har ila yau, ya shaida wa Kwamitin Sojoji na Majalisar Wakilai cewa za a ƙara kasafin kuɗin Pentagon na shekara mai zuwa inda zai kai adadin da bai taɓa kasancewa ba na dala tiriliyan 1.5.