'Yan awaren Yemen sun ayyana sabon kundin tsarin mulkinsu
January 3, 2026
'Yan awaren Yemen da ke ikirarin ballewa daga kasar, sun ayyana sabon kundin tsarin mulkin kudancin kasar, a daidai lokacin da zaman tankiya ke kara zafafa tsakanin Saudi Arebiya da Hadaddiyar Daular Larabawa, wadanda ke zama kasashe mafiya karfi a yankin Gulf.
A wannan Asabar Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da kammala janye dukkan dakarunta daga Yemen, kamar yadda ta alkawarta, bayan Saudi Arebiya ta zarge ta da marawa 'yan aware baya, tare da tallafa musu da makaman yaki.
Ko a ranar Juma'a sai da Saudi Arebiya ta kai harin bama-bamai da jiragen yaki cikin Yemen, bayan wadanda ta kai a cikin mako, a kokarinta na karya lagon 'yan awaren, wadanda kuma a gefe guda ke adawa da gwamnatin 'yan tawayen Houthi.
Karin bayani: Saudi Arebiya ta kai harin bama-bamai birnin Mukalla a Yemen
A wani ci gaban kuma, Saudi Arebiya ta gayyaci jagororin 'yan awaren, domin halartar taron tattaunawar sulhu a birnin Riyadh, domin warware takaddamar da ta kunno kai, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta sanar ranar Asabar.