1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yan ta'adda sun kashe mutane sama da 127 a Nijar - HRW

September 10, 2025

Human Rights Watch ta bukaci gwamnatin Jihar da ta gudanar da bincike tare da hukunta wadanda aka samu da aikata laifukan yaki da kuma cin zarafin bil Adama a kasar.

https://p.dw.com/p/50Fpp
	
Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani
Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: Télé Sahel/AFP

Kungiyar  Human Rights Watch ta ce mutane sama da 127 suka rasa rayukansu a Jamhuriyar Nijar samakamon hare-haren kungiyoyin masu ikrarin jihadi tun daga watan Maris na 2025.

Karin bayani:'Yan ta'adda sun kashe sojoji a Jamhuriyar Nijar

Kungiyar da ta himmatu wajen kare hakkin bin Adama a duniya ta ce lamarin ya fi kamari a yankin Tillaberi da ke kan iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso. Sai dai, gwamnatin Nijar dai ba ta mai da martani ba kan rahoton na Human Rights Watch ba.

Karin bayani:Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Tillaberi na Nijar

Sojoji sun hambarar da gwamnatin farar hula a kasar ta Nijar a 2023, inda suka kafa hujja da rashin tsaro da yaki ci yaki cinyawa a kasar da ke yammacin Afrika, tare kuma da korar dakarun Faransa da Amurka da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar. Nijar dai ba da maida martani kan rayukan fararen hula da aka kashe a kasar ba.