Ziyarar shugaban China a Koriya ta Arewa
June 9, 2026
Shugaba Xi Jinping na China ya sauka filin jirgin saman Pyongyang domin gudanar da ziyarar aiki da ke zama ta farko cikin shekaru bakwai a Koriya ta Arewa. An dai kawata babban birnin Koriya ta Arewa, inda kan manyan tituna aka sanya tutocin kasashen biyu, da hotunan Xi Jinping da na Kim Jong-Un.
Tasirin ziyarar
Ziyarar Xi Jinping na da matukar muhimmanci ga shugaban Koriya ta Arewa, saboda haka ne Kim Jong-un ya tanadi goma ta arziki don mutunta bakonsa, in ji John Delury, kwararre a cibiyar Asia Society, a wata hira da ya yi da Reuters ya nuna cewa ga Kim Jong Un, karbar bakuncin daya daga cikin shugabannin duniya mafi karfi, watakila wanda karfinsa ya yi daidai da Donald Trump na Amurka, wata babbar nasara ce. Kim Jong Un zai iya amfani da wannan ziyara a matsayin farfaganda a cikin gida.
Xi Jinping ba zai je Koriya ta Arewa don faranta wa takwaran aikin Kim Jong-Un rai ba ne kawai, a'a. Saboda hake ne mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta bayyana manufofin da Xi ke neman cimma na karfafa alaka tsakaninsu, kafin ya isa Koriya ta Arewa game da batutuwan da suka shafi kasashen biyu.
Kafin ma ya fara wannan ziyarar, Shugaba Xi da kansa ya jaddada abota mai dorewa tsakanin kasarsa da Koriya ta Arewa. A cikin wani sharhi da ya yi a wata jaridar Koriya ta Arewa, ya yi magana game da sabbin damarmakin ci gaba da kasashen biyu makwaftan juna za su amfana da su.
Masu nazarin harkokin yau da kullum
Masu sharhi suka ce wannan yana nufin cewar za a samu hadin gwiwa mai karfi a fannin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Dama Koriya ta Arewa na niyyar fara wani shiri na shekaru biyar wanda ya hada da farfado da yawon bude ido a kasar. Idan za a iya tunawa dai, kafin rufe iyakokinta sakamakon barkewar annobar Corona a farkon shekarar 2020, 'yan yawon bude ido na kasar Sin ne suka fi ziyartar kasar.
Tun bayan yakin Koriya a farkon shekarun 1950 ne, China ta kasance abokiyar huldar siyasa da tattalin arziki mafi muhimmanci ga Koriya ta Arewa. An sanya takunkumai da dama ga Koriya ta Arewa saboda shirinta na makamai masu linzami da makaman nukiliya. Sai dai a baya bayan nan, kasar da ke zama saniyar ware a duniya ta kara karfafa alakarta da Rasha, inda ta tura da gudunmawar sojoji a yakin da Rasha ke yi da Ukraine.
A cewar kwararre kan harkokin Koriya ta Arewa John Delury, ziyarar farko ta kasar Sin a wannan shekarar tana da wata manufa.
Xi Jinping na son gane wa idanunsa zahirin abin da ke faruwa a Pyongyang, kuma daga cikin wuraren da zai ziyarta har da fadar Kumsusan da ke dauke da kabarin Kim Il-sung da Kim Jong-il.
Bayan wannan, babu sahihan bayanai kan ainihin jadawalin ziyarar kwana biyu da Xi jinping ke yi a Koriya ta Arewa, saboda ba a yarda kafofin watsa labarai na kasashen waje masu zaman kansu su shiga kasar ba.