1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Al-Sharaa na Siriya na ziyara a Amurka

November 9, 2025

Wannan ita ce ziyara ta farko da wani shugaban Siriya ya kai Amurka tun bayan samun 'yancin kan kasar a 1946.

https://p.dw.com/p/53Kqq
Wannan ita ce ganawa ta biyu da Donald Trump ya yi da Ahmad al-Sharaa
Wannan ita ce ganawa ta biyu da Donald Trump ya yi da Ahmad al-SharaaHoto: Bandar Aljaloud/Saudi Royal Palace/AP Photo/picture alliance

Shugaban Siriya Ahmed al-Shara, ya isa Amurka a wata ziyarar aiki ta tarihi, in ji kamfanin dillancin labaran kasar.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da Washington ta cire sunansa daga jerin masu tallafa wa ta’addanci.

Kasar Siriya na son sake fasalta dangantakarta da Rasha

Al-Sharaa, wanda mayakansa suka kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad a shekarar da ta gabata, zai gana da shugaban Amurka Donald Trump a fadar White House ranar Litinin.

Masana na cewa wannan shi ne karo na farko da wani shugaban kasar Siriya ya kai ziyara Amurka tun bayan samun 'yancin kan kasar a 1946.

Trump da al-Sharaa za su yi ganawar keke da keke

Shugaban ya fara ganawa da Trump a birnin Riyadh a lokacin ziyarar shugaban Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya a cikin watan Mayun 2025.