1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Amurka ta gargadi China kan yi wa Taiwan barazanar soji

January 2, 2026

Amurka ta bayyana atisayen sojoji da China ta yi a baya-bayan nan a kusa da Taiwan a matsayin abin damuwa da kuma bai dace ba.

https://p.dw.com/p/56DXZ
Atisayen sojin China a kusa da Taiwan
Atisayen sojin China a kusa da TaiwanHoto: Eastern Theatre Command/REUTERS

Kakakin ma'aikatar harkakin wajen Amurka Tommy Pigott ya fitar da sanarwa a ranar Alhamis, wadda a cikinta Washington ta yi kiran Beijing da ta kai zuciya nesa tare da dakatar da barazanar soji da take yi wa Taiwan.

Sanarwar ta bayyana atisayen sojoji da China ta yi a baya-bayan nan a kusa da Taiwan a matsayin abin da ke kara rura tada jiyoyin wuya, sannan kuma ta shawarci Beijing ta hau tebirin tattaunawa da mahukutan Taiwan.

Har wa yau Washington ta ce tana goyon bayan zaman lafiya a mashigin tekun Taiwan, kana kuma tana adawa da duk wani yin gaban kai ta hanyar barazanar soji ko kuma matsin lamba.

China dai da ke ikirarin cewa tsibirin Taiwan wani yanki ne na kasarta, ta gudanar da gagarumin atisayen soji a farko da tsakiyar wannan mako, lamarin da shugaban Amurka Donald Trump ta bayyana a matsayin abin damuwa.