1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Hankalin 'yan Najeriya ya rabu gida biyu kan sake cin bashi

Uwais Abubakar Idris MAB
April 1, 2026

Majalisar dattawa ta amincewa Shugaba Bola Tinubu ya karbo bashin Dalla bilyan shida a daidai lokacin da ake nuna damuwa a kan karuwar bashin da ake bin Najeriya da kuma rashin aiwatar da kasafin kudi.

https://p.dw.com/p/5BVxJ
Nigeria Änderung der Wähung Naira
Hoto: Ubale Musa/DW

Majalisar dattawa ta Najeriya ta kara yawan kasafin kudin 2026 da ta amince da shi wanda a yanzu ya kai Naira tirliyan 68.323. Sannan ta amince wa shugaban Najeriyar Bola Tinubu na karbo Karin bashi na Dalla bilyan shida bayan da ta yi muhawara a zama na musamman da ta yi a Abuja. Gwamnati ta bayyana sabon bashin a matsayin ci gaba da aiwatar da muhimman ayyuka da jama'a ke bukata a Najeriya.

Sai dai, kwararu sun fara daga ‘yar yatsa a kan yawan bashin da Najeriya ke karbowa saboda tana kashe kusan kashi 60% na kudadden da take samu wajen biyan bashi. Wannan na zuwa a lokaci da Najeriyar ta bi sahun kasashen da suke cin moriyar garabasa ta tsadar da gurbataccen man fetur ke yi a duniya saboda yakin da ake yi a kasar Iran.

Karinn bayani:  Kasafin kudin Najeriya ya janyo cece-kuce

Shugaba Tinubu ya aiwatar da kasafin 2026 ba tare da kammala aiwatar da na 2025 ba
Shugaba Tinubu ya aiwatar da kasafin 2026 ba tare da kammala aiwatar da na 2025 baHoto: Ubale Musa/DW

 
 
Dr Isa Abdullahi, masanin tattalin arziki ne da ke Najeriya ya ce: "Wadannan bashusshuka na dada yin yawa ga kasa, kuma suna nema su ci karfin kasa. Ita gwamnati tunaninta shi ne a karbo tun da wannan kason na cikin bashi, abin da ya samu na rara kuma a ajiye." 

Kwararru na bayyana bukatar tsumi a irin wannan lokaci da Najeriya ta samun karin kudadden shiga, maimakon kasaftawa da kashe su, kamar yadda Sanata Ahmed Babba Kaita, dan jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya ya bayyana.

A daya hannun kuma, majalisar dokokin Najeriyar ta amince da kasafin kudin Najeriyar na 2026 inda a nan ma ta kara yawansa da Naira Tirliyan 9, Wannan ya nuna cewar kasafin kudin ya karu daga Naira tirliyan 58.4 zuwa tirliyan 68.3.  Sanata Yahya Abdullahi na cikin 'yan majalisar dattawa da suka amince da kasafin kudin, ya bayyana dalilansu. Ya ce: "Abin da ya faru shi ne, bayan da shugaban kasa ya kawo kasafin kudi na farko, daga baya wasu larurori sun shigo. Akwai 'yan kwangila da suka yi ayyuka suna tsaya a gaban ma'aikatar kudi inda suke zanga-zanga.

Karin bayani: Najeriya: Ina rarar kudin mai suka shiga?

Majalisar dattawa ta sake amince da kudirin gwamnatin Tinubu na ciwo bashi
Majalisar dattawa ta sake amince da kudirin gwamnatin Tinubu na ciwo bashiHoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

  Abin da ya fi daukar hankali a batun kasafin kudin shi ne rashin aiwatar da shi sau da kafa, inda bayanai suka nuna cewar a 2025 ma'aikatu da dama ba'a saka masu kudadden gudanar da muhimman ayyukansu ba.  Abubakar Ali, masanin tattalin arziki da ke Abuja ya ce: "Aiwatar da kasafin kudi na wannan gwamnati abin al'ajabi ne, kuma abin ban haushi ne, domin duk kudirin da majalisar dattawa ta samu daga shugaban kasa tana saurin amincewa da shi. A cikin awa hudu ta amince da wannan kudirin doka"

Najeriya na kokarin warware rikita-rikitar aiwatar da kasafin kudi inda ta amince a ci gaba da aiwatar kasasfin kudin shekarar 2025.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani