1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Me tsadar mai za ta haifar a Najeriya?

April 16, 2026

A wani abun da ke iya kai Tarayyar Najeriya cikin rudani, masu kamfanonin jiragen sama a kasar sun ce suna shirin ajiye jiragensu daga Litinin din mako mai zuwa 20 ga watan Afrilun 2026.

https://p.dw.com/p/5CItI
Najeriya | Man Fetur | Tsada | Jiragen Sama | Dakatar da Aiki
Filayen jiragen sama na shirin zama fanko a Najeriya, saboda tsadar maiHoto: Osodi Emmanuel/IMAGO

Tsadar farashin man jirgin ne dai, ya kai tunanin hutun da ke iya shafar sufurin na sama  abun alfaharin 'yan bokon Najeriyar. Duk da matatar Dangote dai, man ya tashi daga Naira 900 kan kowace lita ya zuwa Naira 3,300 a halin yanzu. A kusan kullum jiragen saman da ke kai kawo a cikin Tarayyar Najeriya, na shan abun da ya kai lita miliyan biyu na man jirgin a kai kawon da suke cikin kasar da jirgin na sama ke zaman hanya mafi farin jini tsakanin 'yan boko.

Kara kudin tikiti ko tafka asara?

To sai dai kuma tashi cikin farashin man yanzu haka, na neman jefa daukacin masana'antar jiragen na sama da ke a Najeriyar cikin rudani. Kungiyar mamallaka jiragen na sama da ke a kasar ta ce tana shirin ta tsaida ayyukan jiragenta, sakamakon tashi irin na gwauron zabi cikin farashin man jirgin. Farashin man dai ya tashi daga Naira 900 kan kowace lita cikin watan Fabrairun da ya shude, ya zuwa Naira 3,300 a halin yanzu.

Karin Bayani: 

Najeriya: Ko matatar Dangoto za ta taimaka?

Abun kuma da ya kai ga sabuwar barazana cikin masana'antar, wacce ke tsakanin kara kudin tikitin jirgin da asarar mafi yawa na fasinjojinta. Dama dai an dauki lokaci ana nunin yatsa kan tsadar tikitin, kafin sabon karin da masu jirgin suke fadin ya yi kama da kokarin samun riba ta haramun. Mamallaka jiragen saman sun ce, ko dai masu sai da man su rage farashi ko kuma jirage su tsaya sai abun da hali ya yi.

Najeriya | Kamfanin Man Fetur | NNPC | Abuja
Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCHoto: Reuters/A. Sotunde

Ibrahim Shehu dai na sharhi cikin batun makamashi kuma yace, rikicin makamashin na zaman ruwan dare gama duniya a wannan lokaci. Kafin tashi cikin farashin man dai, kudin man jirgin kan dauki abun da ya kai kusan kaso 40 cikin 100 na daukacin bukata ta jiragen. Kuma bayan karin masu jiragen sun ce, daukacin kudin shigar da suke samu ba ya iya biyan sabon farashin man jirgin.

Akwai rarrabuwar kawuna

Majiyoyi cikin masana'antar sun ce, a daukacin watan Maris na 2026 matatar Dangoten da ke zaman abun alfahari cikin kasar a halin yanzu ba ta bai wa jiragen Najeriyar ko da digon man ba. To sai dai kuma, sabuwar barazanar na neman raba kawunan masu ruwa da tsaki da ke cikin masana'antar. Wannan ne dai karo na farko da jirage ke shirin tafiya hutu, a cikin kasar da ke dada fuskantar rashin tsaro ta ko'ina.

Karin Bayani: 

Hira da Alhaji Aliko Dangote

Kyaftin Ado Sunusi na zaman shugaba na kamfanin Euro Contractors, kamfani mafi dadewa a cikin masana'antar yanzu. A cewarsa, ba hujjar tsayar da ayyukan jiragen saboda tsadar man jirgin. Fasinjoji tsakanin miliyan 11 zuwa 13 ne dai, jiragen kan dauka a shekara cikin kasar da ke zaman mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Edited and published by Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani