1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiJamus

Zabtare hasashen bunkasan tattalin arzikin Jamus

Suleiman Babayo ZUD
April 22, 2026

Sakamakon yakin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya wanda ya haifar da matsalolin makamashi an zabtare hasashen samun samun bunkasan tattalin arzikin kasar Jamus a wannan shekara ta 2026.

https://p.dw.com/p/5Cfl5
Katherina Reiche ministar kula da tattalin arzikin Jamus
Katherina Reiche ministar kula da tattalin arzikin Jamus Hoto: To bias S ch warz/AFP

Gwamnatin Jamus ta zabtare hasashen yuwuwar samun bunkasan tattalin arzikin kasar zuwa habaka na kaso 0.5 cikin 100 a wannan shekara ta 2026, sakamakon tashin farashin makamashi da duniya ke fuskanta, tun lokacin da yaki ya barke a yankin Gabas ta Tsakiya, inda kasashen Amurka da Isra'ila suka kaddamar da farmaki kan kasar Iran.

Dalilan zabtare hasashen

Ministar kula da tattalin arziki ta kasar, Katherina Reiche ta bayyana haka a wannan Laraba lokacin da ta gabatar da sabon hasashen, wanda ya saba wanda aka gabatar tun farko na samun bunkasa da kaso 1 cikin 100, inda yanzu aka zabtare rabi kididdigar da aka fara yi, saboda tashin farashin makamashin man fetur da duniya ke fuskanta, tun lokacin da yakin na Gabas ta Tsakiya ya barke tare da haifar da rashin tabbas a kasuwannin duniya.

A baya annobar cutar Covid-19 da yakin tsakanin Rasha da Ukraine duk sun taimaka wajen kassara bunkasan tattalin arzikin kasar ta Jamus, wadda take sahun gaba na kasahen masu karfin tattalin arziki a duniya, inda take matsayi na uku bayan kasashen Amurka da China.