1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiJamus

Barazanar yajin aiki a kamfani Lufthansa

Suleiman Babayo ZUD
February 11, 2026

Kamfanin sufurin jiragen saman Jamus na Lufthansa ya caccaki matsayin kungiyar matuka jiragen.

https://p.dw.com/p/58YHh
Kamfanin sufurin jiragen saman Jamus na Lufthansa
Kamfanin sufurin jiragen saman Jamus na LufthansaHoto: Frank Hoermann/SVEN SIMON/picture alliance

Kamfanin sufurin jiragen saman Jamus na Lufthansa ya caccaki matsayin kungiyar matuka jiragen na shirin shiga yajin aiki ranar Alhamis, ganin cewa kungiyar tana sane da cewa kamfanin ba yi da kudin da suke bukata.

Kamfanin sufurin jiragen saman Jamus na Lufthansa
Kamfanin sufurin jiragen saman Jamus na LufthansaHoto: Sven Hoppe/dpa/picture alliance

Ita dai kungiyar ta kira yajin aikin kwana guda na matuka jiragen saman kamfanin na Lufthansa, saboda takaddama kan kudin fansho.

Muddun matuka jiragen saman kamfanin na Lufthansa suna shiga yajin aikin na wannan Alhamis, haka zai shafi tafiye-tafiye dubban fasinjojin da suke tafiya tare da kamfanin na Lufthansa.