Jamus ta bai wa rabin 'yan gudun hijiran Ukraine aiki
February 17, 2026
Rabin 'yan kasar Ukraine da suka tsere zuwa Jamus a watanni shida na farkon yaƙi da Rasha sun samu aiki bayan shekaru uku da rabi.
Wani rahoto da hukumomin kula da kaurar jama'a da na aikin yi a Jamus ne suka fadi hakana ranar Talata.
Shugaban Jamus na ziyarar Spain kan halin da Ukraine ke ciki
Rahoton ya kuma nuna har yanzu adadin ’yan Ukraine masu aiki ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da jimillar al’ummar da ke bukatar aiki wanda ya kai kusan kashi 68 cikin dari a watan Yunin 2025.
Saboda takunkumin tafiye-tafiye da aka kakaba wa mazan da ake iya tura su soja, yawancin 'yan gudun hijiran mata ne da ke kula da 'ya'yansu su kadai.
Jamus ta shirya mika kadarorin Rasha da ke hannun wa Ukraine
A watan Satumban 2025, kashi 21 cikin dari ne kawai na matan Ukraine masu 'ya'ya kanana da shekarunsu bai wuce uku ba kuma ba su da abokin zama, ke aiki, in ji rahoton.