Nijar: Ko harin Mali zai zama ishara?
April 28, 2026
Jamhuriyar Nijar dai ta bayyana cewa, tsaurara matakan tsaron da kuma yin kira ga al'umma su sanya idanu sosai ne ya kamata a bai wa karfi da nufin kaucewa fuskantar irin matsalar da makwabciyarta Mali ta samu ta harin 'yan ta'adda. Tun dai da jimawa hukumomi a Nijar suka dauki matakan tsaurara tsaron, ganin cewa ita ma ta fuskanci harin ba-zata na 'yan ta'adda a barakin sojojin samanta da ke filin jiragen sama. Tun daga wancan lokaci hukumomin tsaro da ma al'umma ke ci gaba da buda idanunsu da kuma leka ko'ina, domin ganin harin bai sake faruwa ba.
Idan gemun dan uwanka ya kamata da wuta.....
Wannnan hari na baya-bayan nan da aka kai a Mali, ya kara zaburar da hukumomin da ma al'umma kan matakan da ya kamata a dauka. A cewar Houssei Maizoumbou mai fafutukar neman 'yancin Nijar, duk wanda ya bayar da gudunmawa ta kariya kansa ya yi wa idan har yana kishin kasarsa. Da yake magana kan wannan batu Oumarou Souley na kungiyar FCR mai fafutukar kare hakkin dan Adam ya ce, sun yi imanin gwamnatin Nijar za ta bi diddigin abubuwan da suka faru a Mali da duk wadanda suke da hannu cikin lamarin. A cewarsa daga nan ya kamata ta dora nata matakan da tuni ta dauka na bayar da kariya ga al'umma da sauran manyan ma'aikatun kasar.
Tun da jimawa mutane da dama sun nemi a koma karkashion tsohon tsarin tsaro na daga tushe, kuma da yake magana tare da bayar da shawarwari kan matakan dauka, Dakta Atto Namaiwa Malami a jami'ar birnin Tahoua a Jamhuriyar Nijar din na ganin sai an koma kan fasaha ta lokacin juyin mulki na farko a Nijar. Magabatan wancan lokaci, sun tsara al'umma tun daga mataki na unguwa da garuruwa da gundumomi da masarautun gargajiya zuwa jihohi. Ya ce a samu jagorori da al'umma take ganin kimarsu, domin ba su labarin abun da suka gani mai kyau ko maras kyau su kuma su isar da sako zuwa sama.
Kwadayi ko rashin kishin kasa?
Babban abun da ke daukar kankali dai shi ne, yadda ake samun mutanen cikin garuruwa ko kauyuka duk da matakan da ake dauka na tsaro da fadakarwa su kokarinsu shi ne abun da za su samu ta fuskar abun duniya. Ana zargin cewa, ana hada baki da wasu wajen shigo da 'yan ta'adda wasu kuma na bin duk hanyoyin da za su bi wajen kai musu mai da magunguna ko abinci.
Edited and Published by Lateefa Mustapha Ja'afar