1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamin roka na dogon zango

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 29, 2026

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya kai ziyara cibiyar horas da jami'ai na musamman dabarun kwarewa a kan yaki.

https://p.dw.com/p/5BKf3
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un tare da 'yarsa Kim Ju Ae
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un tare da 'yarsa Kim Ju AeHoto: KCNA/REUTERS

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya jagoranci gwajin wani makamin roka mai cin dogon zango, a kokarin kasar na ci gaba da karfafa makamanta.

Gwajin na zama wani bangare na jadawalin shekaru biyar da Pyongyang ta tsara, don cimma wani fage na karfafa tsaro.

Karin bayani: Ba za mu dena kera nuclear ba - Kim

Haka zalika shugaban ya kai ziyara cibiyar horas da jami'an tsaro na musamman a kasar, wadanda ke samun kwarewa a kan yaki.