1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Mace ta farko ta dauko hanyar zama Firaminista a Japan

October 4, 2025

A karon farko a tarihin Japan za a zabi mace daga jam'iyyar Liberal a matsayin wacce za ta iya zama sabuwar Firaminista.

https://p.dw.com/p/51UAB
Sanae Takaichi
Sanae Takaichi Hoto: Kim Kyung-Hoon/POOL/AFP/Getty Images

Wakilai sama da dubu 900,00 suka kada kuri'a ciki har da wakilan jam'iyyar Liberal Democratic Party 295 da suka kada kuri'a ga mai ra'ayin 'yan mazan jiyan nan Sanae Takaichi, a gayaye na biyu bayan ta fafata da Shinjirō Koizumi wanda ya samu kuri'u 156.

Karin bayani:An fara takarar neman maye gurbin firaministan Japan

Takaichi na daya daga cikin makusanta kuma masu ra'ayin 'yan mazan jiya na tsohon firaministan kasar Shinzo Abe, wanda aka halaka shi a bainar jama'a a lokacin da yake wani gangami a 2022.