1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Obama ya soki kashe masu zanga-zanga a Amurka

January 26, 2026

Tsoffin shugabannin kasar Amurka irin Barack Obama da Bill Clinton sun ce ba za su lamunci kashe masu bore ba, a daidai lokacin da jami'an ICE suka kashe mutum na biyu.

https://p.dw.com/p/57Reo
Tsohon shugaban Amurka, Barack Obama
Tsohon shugaban Amurka, Barack ObamaHoto: Brynn Anderson/AP/dpa/picture alliance

A daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar kin jinin ma'aikatan hukumar shige da fice da fasakauri a Amurka, tsofaffin shugabannin kasar Barack Obama da Bill Clinton sun bukaci gwamnatin Donald Trump da ta yi gaggawar kawo karshen bude wuta kan masu zanga-zangar, kiran na zuwa a daidai lokacin da jami'an ICE suka kashe mutum na biyu a Minneapolis.

Karin bayani:Jami'an Amurka sun harbe wani mutum har lahira

Gwamnatin Trump na fuskantar matsin lamba kan shirinta na murkushe masu zanga-zangar adawa da cafke 'yan ci rani da bakin haure da ma'aikatan ICE ke yi. Jami'an hukumar sun kashe wani matashi mai suna Alex Pretti, 'dan shekara 37, wanda ke zuwa makwanni uku da halaka wata matashiya mai suna Renee Good, 'yar shekara 37, a cikin motarta.

Karin bayani:Trump ya cika shekara guda a kujerar mulkin Amurka

Gwamnatin Trump ta kare matsayarta kan kashe-kashen, inda ta ce matasan sun yi amfani da bindiga kan ma'aikatan na ICE, wanda daga bisani suka yi amfani da karfi wajen maida martani.